22 Oktoba 2021 - 16:05
Ana Taron Samar Da Kwanciyar Hankali A Libiya

A Libiya an bude wani taron kasa da kasa mai manufar tattauna hanyoyin da za’a shinfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wannan shi ne taron ministocin ketare irinsa na farko a Tripoli, inda tawagogi na ministoci daga kasashe kimanin talatin ke halartar taron.

Babban abunda taron ya sanya a gaba shi ne, shirya zaben da ake son gudanarwa a watan Disamba.

Haka kuma batun tsaro, da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma tattalin arziki duk suna cikin batutuwa da za’a tattauna yayin taron.

A kwanan nan Libiya na cikin kwararen matakan tsaro domin tabbatar da tsaro ga mahalarta taron.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta ce, zatayi amfani da wannan damar domin samun tallafin shayo kan matsalolin kasar, ciki har da duba hanyoyin karbo kudadenta kimanin biliyan 170 da kasashen turai da MDD, suke rike da tun cikin shekarar 2011.

Saidai gwamnatin rikon kwaryar ta Tripoli, ta ce tana son karbar kudin ne bayan kafa gwamnatin da aka zaba.

342/